Isa ga babban shafi

Onana na tsaka mai wuya kan zabin zuwa AFCON ko ci gaba da Firimiya

Tsohon dan wasan Manchester United Eric Djemba-Djemba ya shawarci Andre Onana dake cikin tsaka mai wuya da ya yi tunani sosai kan makomarsa a bangren sana’arsa ta tamola.

Golan Manchester United Andre Onana 17 ga Disamba, 2023. (AP Photo/Jon Super)
Golan Manchester United Andre Onana 17 ga Disamba, 2023. (AP Photo/Jon Super) AP - Jon Super
Talla

Andre Onana zai yanke shawarar ko ya rasa wani bangare na gasar Firimiyar Ingila don wakiltar kasarsa Kamaru a gasar cin kofin Afirka da Cote d’Ivoire zata karbi bakwanci a watan Janairu ko kuma ya ci gaba da wasa old trafford.

Mai tsaron ragar Indomitable Lions Onana na iya yin rasa wasannin United na sama da wata guda idan ya zabi zuwa gasar da za a yi a Ivory Coast.

Dan wasan mai shekaru 27, wanda ya kawo karshen ritayar sa na kasa da kasa a watan Satumba, bai takawa Club dinsa United abin a zo a gani ba, a kakar wasa ta bana, wanda hakan ya sa ta fice daga Turai da kuma rashin armashi a wasannin cikin gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.