Isa ga babban shafi
AFCON

Super Eagles ce tawaga mafi tattara zakakuran 'yan wasa a AFCON

Wasu alkaluma da kwararru a bangaren tamaula suka tattara na nuna cewa tun bayan tawagar Najeriya da ta lashe gasar AFCON a 2013 lokacin da Afrka ta kudu ta dauki nauyin gasar, wannan ke karon farko da tawagar ta Super Eagles ke fita gasar da zaratan ‘yan wasan da ake ganin ko dai suyi kankankan ku kuma su iya zartar bajinta takwarorin nasu na shekaru 11 da suka gabata.

Dan wasan gaba na Najeriya Victor Osimhen yayin zura kwallo a ragar Equatorial Guinea.
Dan wasan gaba na Najeriya Victor Osimhen yayin zura kwallo a ragar Equatorial Guinea. AP - Sunday Alamba
Talla

Super Eagles wadda ta lashe kofin na AFCON sau 3 a tarihi, na sahun kasashen da ake yiwa hasashen iya lashe kofin ganin yaddda ta tattara tarin ‘yan wasan da ke taka leda a ketare fiye da kowacce kasa daga nahiyar.

Mai horar da tawagar ta Super Eagles Jose Peseiro ya debi jerin zakakurai kuma zaratan ‘yan wasa a tawagar tasa zuwa Ivory Coast da suka kunshi masu tsaron raga 3, masu tsaron baya 9 da ‘yan wasan tsakiya 5 sai kuma ‘yan wasan gaba guda 8.

A jerin masu tsaron raga akwai Stanley Nwabili na Chippa United kana Francis Uzoho na Omonoia FC kana Olorunleke Ojo na Enyimba.

A bangaren masu tsaron baya akwai William Troost-Ekong na POAK FC sannan Bright Osayi Samuel na Fenerbahce sai Ola Aina na Nottingham Forest tukuna Zaidu Sanusi daga FC Porto kana Bruno Onyemaechi da ke taka leda da Boavista FC.

Sauran sun kunshi Semi Ajayi na West Bromwich Albion sannan Calvin Bassey na Fulham da kuma Chidozie Awaziem na Boavista na FC kana Kenneth Omuero da ke taka leda da Kasimpasa SK.

A bangaren ‘yan wasan tsakiyar na Super Eagles kuwa akwai Frank Onyeka daga Bentford FC da Joseph Ayodele-Aribo daga Southampton sannan Alex Iwobi na Fulham sai Raphael Onyedika da ke taka leda da Club Brugge sannan Alhassan Yusuf na Royal Antwerp.

Jerin ‘yan wasan gaba na Super Eagles din kuwa akwai Kelechi Iheanacho da ke taka leda da Leicester City sai Victor Oshimen na Napoli sannan Terem Moff daga Nice da Samuel Chukwueze daga AC Milan.

Sauran sun kunshi Ademola Lookman da ke taka leda da Atalanta sannan Moses Simon daga Nantes sannan Paul Onuachu daga Trabzonspor sai kuma Ahmed Musa daga Sivasspor.

Binciken kwararrun na baya-bayan nan na nuni da cewa tawagar ta Super Eagle ita ke matsayin tawaga mafi tattara ‘yan wasa masu tsada da daraja a kaf nahiyar Afrika lura da yadda ta ke da wakilci a kusan dukkanin lig-lig din Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.