Isa ga babban shafi
Fadar Vatican

An bukaci sabon Fafaroma ya yi aiki wajen samar da zaman lafiya a duniya

Shugabannin duniya da shugabannin mabiya Darikar Katolika sun yaba da zaben Jorge Bergoglio daga Argentina a matsayin sabon Fafaroma wanda ya gaji Fafaroma Benedict tare da kira ga gare shi ya yi aiki wajen samar da zaman lafiya a Duniya.

La presidenta Kirchner y el cardenal Jorge Bergoglio en la Basílica de Luján, 22 de diciembre de 2008. .
La presidenta Kirchner y el cardenal Jorge Bergoglio en la Basílica de Luján, 22 de diciembre de 2008. . REUTERS/Ezequiel Pontoriero/DyN
Talla

Shugaban Amurka Barack Obama da shugabar Argentina Cristina Kirchner sun mika sakon taya murnarsu a madadin dimbin mabiya darikar Katolika a yankin Amurka.

Dubban mabiya ne a Aregentina suka hada gangami domin murnar zaben Fafaroma Francis wanda shi ne Fafaroma na farko daga yankin Amurka.

A jawabin sabon Fafaroman yace zai ci gaba da aiki inda Fafaroma Benedict ya tsaya wajen kokarin wanzar da zaman lafiya tsakanin mabiya addinin Kirista da sauran Addinai.

Shugabannin kasashen Turai sun mika sakon murna ga sabon Fafaroma inda shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel tace hakkin Miliyoyin Mabiya Katolika ya rataya akan Sabon Fafaroma.

Shugabannin kasashen Brazil da Colombia da Ecuador da Mexico a yankin Latin Amurka sun mika sakon godiya ga shugabannin Katolika da suka zabi Bergoglio a matsayin sabon Fafaroma.

A Nahiyar Afrika, shugaban mabiya darikar a Afrika ta Kudu ya yaba da yadda aka zabi sabon Fafaroma daga yankin Amurka.

Shugaban Mabiyan a Najeriya Archbishop Kaigama yace suna godiya da ganin an zabi sabon Fafaroma tare da alkawalin yin biyayya ga Fafaroma Francis.

Akwai dai babban kalubale da ke gaban sabon Fafaroman wajen yaki da fyade daga wasu limaman Katolika da matsalar cin hanci da rashawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.