Isa ga babban shafi
Sudan

An saki wasu fursunonin siyasa a Sudan

Hukumomi a kasar Sudan sun bayyana sakin wasu fursunonin siyasa su shida a kasar, wannan kuma na zuwa ne kasa da sa’oi 24 bayan Shugaban kasar Omar al – Bashir ya yi alkawarin sakin daukacin fursunonin siyasar dake tsare. Matakin da hukumomin suka dauka ya jawo cecekuce a kasar a yayin da wani bangare na ‘Yan tawaye suka yi na’am da shi wasu kuma suka yi watsi da yunkurin shugaban.  

Shugaban kasar Sudan Omar al-bashir
Shugaban kasar Sudan Omar al-bashir
Talla

Rahotanni sun nuna cewa mutanen shida, wadanda ke tsare na wani tsawon lokaci, sun sami tarbar iyalansu a wajen gidan yarin Arewacin Khartoum.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch, a kwanan nan ta nemi da a gurfanar da mutanen ko kuma a sakesu.

Shugaba al – bashir, a yayin da yake jagorantar wani taro a Majalisar kasar a ranar Litinin, ya yi alkwarin sakin dukkanin fursunonin siyasar kasar a wani matakin na bude hanyoyin tattaunawa domin a kawo karshe rikicin da kasar ke fama da shi.

Sai dai ‘yan adawa a kasar ta Sudan sun zuba ido su ga ko za a sako fursunoni daga ‘yan tawayen na Sudan Liberation Army Movement.

A da gwamnatin Omar al-bashir ta ki amincewa da tattaunawa da masu tad a kayar baya a matsayin hanyar kawo karshen rikicin na Sudan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.