Saurez zai fuskanci fushin hukuma bayan ya ciji Ivanovic
Dan wasan Liverpool, Luis Saurez, ya nuna nadamarsa bayan ya ciji dan wasan Chelsea, Branislav Ivanovic a karawar da suka yi a jiya inda aka ta shi da ci 2-2.
Wallafawa ranar:
Lamarin dai ya auku ne bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, wanda hakan ya sa Suarez ya bayyana ta kafar sadarwa ta Twitter cewa ya kira Ivanovic a wayar talho ya bashi hakuri.
Har ila yau Saurez ya bawa ‘yan club dinsa hakuri saboda wannan abun kunya da ya yi, inda mai horar da su, Brendan Rodgers ana shi bangaren ya ce, ya nunawa Suarez cewa lallai bai kyauta ba.
A yanzu haka Suarez zai fuskanci tuhuma akan wannan cizo da ya yi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu