Ronaldo ya dawo daga jinya domin karawa da Dortmund
Dan wasan Real Madrid, Cristiano Ronaldo ya dawo cikin abokanan wasansa bayan ya gama murmurewa daga wani rauni da ya ji a wasan da kungiyar kwallon kafa ta Madrid ta yi da Borussia Dortmund a makon da ya gabata. Wannan dawowa da Ronaldo ya yi, na zuwa ne a dai dai lokacin da kungiyarsa ta Real Madrid ke shirin karawa a zagaye na biyu a yau a wasan daf da na karshe na gasar Zakarun Turai na Champions League da aka fara bugawa a makon da ya gabata, inda Dortmund ta lallasa Real Madrid da ci 4-1.
Wallafawa ranar:
A da dai ana ta rade redin cewa Ronaldo ba zai samu buga wasan ba, amma tuni rahotanni suka nuna cewa har ya halarci atisayen da aka yi a jiya Litinin, wanda hakan ke nuna cewa da shi za a fafata a karwar ta yau.
Sai dai masu sharhi na ganin cewa Real Madrid na da babban kalubale wajen ganin ta cika burinta na farke kwallaye hudu da aka zira mata a makon da ya gabata.
Rabon dai da real ta lashe kofin gasar tun a shekarar 2002, kuma sau tara tana lashe kofin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu