FIFA
Tsohon shugaban FIFA Havelange ya yi murabus daga mukaminsa na uban hukumar
Shugaban ko kuma uban Hukumar kwallon kafar duniya ta FIFA, Joao Havelange ya ajiye aikinsa bayan wani rahoto ya nuna cewa Havalange ya karbi miliyoyin kudade na dalar Amurka a matsayin cin hanci a lokacin shirya gasar cin kofin duniya.
Wallafawa ranar:
Talla
Sai dai rahotan ya wanke zargin da akewa Shugaban hukumar mai ci a yanzu, wato Sepp Blatter na karbar kudaden.
Amma Havelange wanda ya jagoranci hukumar a tsakanin shekarun 1974 zuwa 1998 an same shi da laifin karbar kudaden tare da wani sirikinsa, Ricardo Teixera ba ta hanyoyin da suka dace ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu