Isa ga babban shafi
COMORES

Za a sake zaben kasar Comoros

Kotun fasalta kudin tsarin mulkin tsibiri Comores a jiya asabar ta umurci gani an sake gudanar da zaben shugaban kasar a wasu yankunan kasar 13.

Azali Assoumani, dan takara a zaben Shugabancin kasar Comoros
Azali Assoumani, dan takara a zaben Shugabancin kasar Comoros RFI
Talla

Yankunan 13 kamar dai yada kotun ta tabbatar zaben na ranar 10 ga watan Afrilu na tattare da kuskure.
Shugaban kotun Loutfi Soulaiman ne ya sanya hanu a takardar dake kira zuwa shugabanin da nauyi ya rataya a wuyan su na ganin sun bayar da hadin kai wajen shirya sabon zaben.

Sai dai bangaren Shugaban kasar tsohon soji kanal Azali Assoumani wanda aka bayyana cewa ya lashe zaben a baya, sake gudanar da zabe a wasu yankunan zai iya kawo cikas a salon siyasa.
Kanal Azali Assoumani ya samu kashi 40.98 na kuri'u yayinda Mohammed Ali Soilihi na biyu ya samu kashi 39.87 cikin kuri'u sai na uku Gwamnan babban tsibiri Comoros Mouigni Baraka mutumin da ya samu kashi 19.15 cikin dari na kuri'u .
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.