Isa ga babban shafi
equatorial Guinea

E.Guinea ta soki Faransa akan Obiang

Kotun Majalisar Dinkin Duniya ta soma sauraren kara akan zarge zargen rashawa da Faransa ke yi wa Teodorin Obiang mataimakin shugaban Equatorial Guinea wanda da ne ga shugaban kasar.

Teodorin Obiang, Mataimakin Shugaban Equatorial Guinea
Teodorin Obiang, Mataimakin Shugaban Equatorial Guinea Photo: AFP/Abdelhak Senna
Talla

Gwamnatin Equatorial Guinea na son kotun ta janye zarge zargen ne na rashawa da facaka da kudaden jama’a da Faransa ke yi wa dandan Shugaban kasar.

Faransa na zargin Teodorin Obiang ne da laifin almubazzaranci da miliyoyan kudaden jama’a a Equatorial Guinea inda a ranar 24 ga wannan watan na Oktoba ake sa ran zai gurfana gaban kotun Paris.

Amma Gwamnatin Equatorial Guinea na ganin wannan cin mutunci ne daga Faransa.

Akan haka ne gwamnatin ta bukaci Kotun Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da zarge-zargen da Faransa ke yi wa mataimakin shugaban kasa Teodorin Obiang.

Mahaifin shi Teodoro Obiang Nguema ne shugaban kasa kuma a watan Yuni ne ya zabi dan sa Teodorin Obiang A matsayin mataimaki.

Lauyan da ke kare Obiang ya ce zargin Faransa zai cutar da Equatorial Guinea da huldarda da kasashen duniya.

Faransa dai ta kwace wasu kadarorin Obiang a Paris kuma ko wane lokaci tana iya gabatar da sammacin kamo shi, matakin da ya hana wa mataimakin shugaban kasar fita zuwa kasashen waje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.