Ana zaben 'Yan Majalisu a Gambia
Al’ummar Gambia na gudanar da zaben ‘yan majalisu a karon farko tun bayan kawar da gwamnatin Yahya Jammeh da ya shafe shekaru 22 kan karagar mulki. A lokacin mulkinsa, Jammeh kan yi biris da majalisar kasar, in da ya ke kafa dokokinsa ba tare da tuntubar su ba.
Wallafawa ranar:
Sama da mutane dubu 880 ke da damar kara kuri’a a zaben da aka soma tun da misalin karfe 8 na safe agogon GMT.
Zaben wani gwaji ne ga jami’iyyun adawa da dama da suka hada kai wajen kawar da gwamnati Jammeh a watan Disamba bara, kuma sabanin cikin gida da aka samu tsakanin wadannan jam’iyyu bayan rantsar da shugaba Adama Barrow ya nuna cewa kowa ta kansa ya ke a zaben na yau.
Jam’iyyu 9 ne ke takarar, ciki har da ta Jammeh da Jam’iyyar UDP da sarakuna ke da karfi a ciki.
Majalisar kasar na da kujeru 53, sai dai an samu karin 5 kan wanda ake da su a 2012.
Tsawon shekarun da Jammeh ya yi ya na tafiyar da kasar, babu batun bai wa ‘yan majalisu fifiko, sai dai a wannan lokaci Adama Barrow ya sauya wannan al’ada.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu