rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Hakkin Mata Hakkin Dan Adam

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Jamhuriyyar Congo: Sojoji sun kaddamar da sabon salon cin zarafi

media
Wasu magoya bayan jam'iyyun adawa a jamhuriyyar Congo da ke zanga zangar neman shugaban kasa Joseph Kabila ya sauka daga mukaminsa a birnin kinshasa. Reuters/ File

Amurka ta sanar da samun rahotannin sirri da ke cewa sojin Jamhuriyyar Dimokaradiyyar Congo, sun kaddamar da kisan gilla kan fararen hula musamman mata da kananan tare da yi musu fyade, a yankin Kasai.


Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin duniya, Nikki Haley ce ta bada tabbacin, yayinda ta gabatar da kudurin neman kwamitin tsaro na majalisar ya dauki mataki kan lamarin cikin gaggawa.

Har yanzu jakadan Jamhuriyyar Congo a majalisar bai ce komai ba dangane da sabon zargin.

A satin da ya gabata wasu kungiyoyin kare hakkin dan’adam, suka bukaci a binciki laifukan take hakkin dan’adam a yankin na Kasai, bayan da aka gano manyan kabur-bura makare da gawarwaki har 42.

Sama da fararen hula miliyan 1 da dubu 300 suka rasa muhallansu a Jamhuriyar Congo, bayan barkewar fada tsakanin sojoji da ‘yan tawaye a watan Agustan da ya gabata.