rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Congo Brazaville Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Gwamnati da ƴan tawayen Congo za su tsagaita wuta

media
Taswirar kasar Congo RFI/Emilie Camjusan

Bayan kwashe watanni ana dauki-ba-daɗi, wata ƙungiyar ƴan tawaye a Congo ta sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ta da gwamnati ƙasar.


Rikicin da aka yi ta fama da shi a yankin Pool da ke kudanci, ya shafi aƙalla mutane 130,000 tare da hana gudanar da zaɓen yanki a watan Yuni.

Wakilan gwamnati ƙarƙashin jagorancin Jean Gustave Ntondo da kuma na ɓangaren ƴan tawayen sun sanya hannu kan yarjejeniyar ce a garin Kinkala, da ke a matsayin cibiyar yankin.

Mai Magana da yawun gwamnati Theirry Moungalla ya ce suna maraba da wannan mataki, musamman ma a lokacin da tattalin arzikin ƙasar ya shiga cikin mawuyacin hali.