rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Mauritania Rashawa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ameena Gurib-Fakim ta Mauritania ta yi murabus

media
Shugabar kasar Mauritania Ameena Gurib-Fakim. google

Shugabar kasar Mauritania Ameena Gurib-Fakim ta yi murabus a yau Asabar bayan da aka zarge da amfani da dukiyar gwamnati wajen bukatun kashin kanta, ko da ya ke dai a tashin farko ta yi tirjiyar ajje aikin na ta kafin daga bisani ta fuskanci matsin lamba.


Lauyan Shugaba Ameena Gurib, Yousouf Mohamed ya sanar da manema labarai cewa shugar ta rubuta takaddar murabus din na ta a yau Asabar amma ba za ta fara aiki nan ta ke ba har sai ranar 23 ga watan nan kamar yadda ta ambata tun da farko.

Tun bayan bankado zargin amfani da kusan Yuro dubu 25 wajen siyan wata sarka da shuga bar ta yi ne, ta ke ci gaba da fuskantar matsin lamba daga kungiyoyin fararen hula 'yan adawa dama daidaikun mutane kan lallai ta ajje aiki.

A makon da ya gabata ne kuma Gurib ta amince da cewa za ta ajje aikin na ta bayan kammala bikin cikar kasar shekaru 50 da samun 'yancin kai.

Sai dai kuma wasu bayanai da suka fita a ranar Larabar da ta gabata sun nuna cewa akwai yiwuwar shugabar na kokarin wanke kan ta daga wancan zargi da nufin ci gaba da jan ragamar kasar, bayan da fadar shugabar ta yi watsi da zarge-zargen.

A cewar Lauyan na ta matsin lambar da ta ke ci gaba da fuskanta 'yan kwanakin nan daga bangarori daban-daban ya tilasta mata dole ta ajje mulkin nata kamar yadda ta ambata tun da farko.

Ameena Gurib-Fakim ita ce shugabar kasa mace ta farko da ta taba jagorantar kasar ta Mauritania.