Isa ga babban shafi
Mali

Mutane 37 sun mutu a Mali bayan wani hari a garin Koulogon

A kasar Mali mutane 37 da akasarin su makiyaya ne suka mutu sakamakon hari da wasu mafarauta suka kai garin Koulogon dake yankin Mopti a tsakiyar kasar.Harin ya wakana ne a kauyen Koulogon inda ake ganin rikici ne tsakanin mazauna kauyen Fulani da yan kabilar Dozos.

Wani kauyen makiyaya a kasar Mali
Wani kauyen makiyaya a kasar Mali © Coralie Pierret / RFI
Talla

A wata sanarwa daga hukumomin kasar ta Mali, maharan saman babura dauke da bidingogi kuma sanye da kayan mafarauta na ”Dozos” suka afkawa mazauna garin na Koulogon da akasarin su makiyaya ne tareda kashe mutane 37.

Maharan sun kashe sarkin garin Koulogon Moussa Diallo da wasu daga cikin mutanen gidan sa.

Gwamnatin Mali ta dau alkawalin dawo da doka da oda a yankin tareda sanar da gudanar da bicinke don gano maharani da suka kitsa wannan hari zuwa garin na Koulogon.

Gwamnatin kasar da kungiyoyi na ci gaba da bayyana alhinin su,tareda yi kira zuwa mazauna yankunan da su daina gudu daga gidajen su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.