rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Habasha

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An soma bincike kan hadarin jirgin Ethiopia

media
Yankin da jirgin saman Habasha na Ethiopian Airlines ya fadi, kimanin kilomita 43 daga babban filin jiragen sama na Bole da ke Habasha. Reuters

An fara gudanar da bincike dangane da musabbabin faruwar hatsarin jirgin saman kamfanin Ethiopian Airlines, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 157.


Jirgin yayi hadari ne bayan tasowa daga birnin Adis-Ababa babban birnin kasar Habasha zuwa Nairobi a kasar Kenya.

Wadanda suka mutu a wannan hadarin, sun fito ne daga kasashe daban daban har 32.

Ministan sufurin kasar Kenya inda ya kamata jirgin ya sauka James Macharia, ya ce a daidai lokacin da ake aikin bincike don gano musabbabin faruwar hatsarin, tuni aka kafa cibiya ta musamman domin kwantar da hankulan iyalan wadanda lamarin ya shafa.

Kafin sanar da faruwar hatsirin dai tuni mutane suka fara isa a filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Nairobi domin tarben ‘yan uwansu.

Bayanai sun tabbatar da cewa jirgin da ya yi hatsarin, bai wuce shekara daya da fara aikin jigilar jama’a ba.