rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Ebola

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugaban Congo ya sha alwashin kawar da Ebola a 2019

media
Shugaban Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo FĂ©lix Tshisekedi. Sumy Sadurni / AFP

Shugaban Jamhuriyar Congo Felix Tshisekedi ya sha alwashin kawar da cutar Ebola daga kasar a karshen wannan shekara.


Alwashin da shugaban ya sha yayin ziyarar da ya kai Jamus, na zuwa ne bayan da aka kaddamar da sabbin magungunan cutar ta Ebola har kashi biyu.

Cikin watan Agustan shekarar bara, annobar ta sake bulla a lardin arewacin Kivu dake Jamhuriyar Congo, daga bisani ta yadu zuwa kudancin lardin na Kivu da kuma Ituri, wadanda ke iyaka da kasashen Uganda, Rwanda da kuma Burundi.

Tun bayan sake bullar tata zuwa wannan lokaci, annobar ta halaka sama da mutane dubu 2.