Isa ga babban shafi
Libya-Turkiya

Libya ta gindaya sharudda kan bukatar tsagaita wuta

Gwamnatin Libya mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya ta ce bazata amince da shirin tsagaita wuta ba har sai Janar Khalifa Haftar ya janye daga yankunan da ya mamaye a baya-bayan nan.

Dakarun gwamnati da ke yaki da dakaru masu biyayya ga Khalifa Haftar mai rike da manyan yankunan kasar Libya.
Dakarun gwamnati da ke yaki da dakaru masu biyayya ga Khalifa Haftar mai rike da manyan yankunan kasar Libya. REUTERS/Ismail Zitouny
Talla

Shugaban gwamnatin ta Libya, Cheif Fayez al-Sarraj ya ce yana maraba da duk wani shirin samar da zaman lafiya a kasar, amma bisa sharadin dole Haftar ya janye jiki daga yankunan da ya kame yana farmakar dakarun gwamnati.

Acewar Sarraj, Haftar ba shi da nufin ja da baya a yakin da ya faro, hasalima yana neman goyon bayan kasashen da za su mara masa wajen hambarar da gwamnati dai dai lokacin da yake samun goyon bayan wasu manyan kasashe da kuma makwabta.

Turai da kasashen Arewacin Afrika sun kaddamar da wani shirin lallama ta fuskar diflomasiyya wajen ganin yaki bai sake barkewa a kasar ba, tare da neman bangarori biyu masu rikici da juna su sasanta.

Cikin watan Aprilun bara ne Haftar ya kaddamar da farmakin yunkurin kwace iko da birnin Tripoli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.