rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iran Yemen Saudiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Iran ta musanta rahotannin tallafawa yan tawayen Houthi

media
Masu zanga-zangar nuna goyan baya zuwa yan tawayen Houthi a Yemen. REUTERS/Naif Rahma

Kasar Iran tayi watsi da zargin cewar tana goyan bayan wargaza kasar Saudi Arabia wajen baiwa yan tawayen Houthi makaman da suke amfani da su wajen kai mata hari.

A baya dai Amurka ta yi barazanar daukar matakai na gaban kan ta a kan Iran


Ko a baya-bayan nan Saudiyya ta gano wasu makamai da 'yan tawayen ke amfani da su wanda ta ke da yakinin cewa Iran ce ta taimaka musu da makaman.

Kasar Iran ta kuma bayyana damuwa kan yadda Saudiya ke hada kai da Amurka da kuma kawayen ta wajen neman ganin bayan Iran.

A wani bicinke daga Majalisar Dinkin Duniya, ta ce akalla kananan yara miliyan 11 ke bukatar agajin gaggawa a kasar Yemen sakamakon halin kuncin da suka shiga saboda yakin da ake gwabzawa a kasar.