Isa ga babban shafi
Morocco

2016 za ta kasance shekarar da aka fi tsananin zafi

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, akwai yiwuwar wannan shekara ta 2016 da ke shirin karewa, ta kasance wadda aka fi tsananin zafi a sakamakon matsalar dumamar yanayi.

A wannan karnin ne aka samu shekaru 16 da aka fi tsananta zafi daga cikin 17
A wannan karnin ne aka samu shekaru 16 da aka fi tsananta zafi daga cikin 17 Reuters
Talla

An fitar da rahoton ne Morocco inda shugabannin kasashen duniya ke tattauna yadda za a magance matsalolin canjin yanayi a duniya.

Rahoton ya ce a cikin wannan karnin ne aka samu shekaru 16 da aka fi tsananta zafi daga cikin 17

Masana kimiya sun ce, har yanzu ana ci gaba da fitar da hayaki mai gurbata muhalli, abin da suka bayyana a matsayin babban musabbabin haifar da dumamar yanayi a duniya.

Majalisar ta Dinkin Duniya ta yi gargadi kan munanan sakamako da sauyin yanayin zai haifar nan gaba, matukar aka gaza magance matsalar.

Masana kimiyar sun ce, matukar kasashen duniya ba su hanzarta rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli ba, to lallai akwai yiwuwar al’ummar duniya za su ci gaba da fuskantar bala’oi da dama da suka hada da fari da ambaliyar ruwa da kuma tsananin zafi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.