Isa ga babban shafi
Amurka

Macron da Trump sun amince da karfafa yarjejeniyar nukiliyar Iran

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takawaransa na Amurka Donald Trump, sun amince da sake karfafa ka’idojin da ke karkashin yarjejeniyar nukiliyar Iran.

Shugaban Amurka Donald Trump, yayin ganawa da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron a birnin New York.
Shugaban Amurka Donald Trump, yayin ganawa da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron a birnin New York. REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Jagororin sun cimma matsayar ce, a ci gaba da ziyarar kwanaki uku da shugaban Faransa Emmanuel Macron ke yi a Amurka.

Sai dai yayin ganawar shugabannin biyu a Amurka, Trump ya kaucewa alkawarin jingine aniyarsa ta janye Amurka daga cikin yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma, tsakanin manyan kasashen duniya da kasar ta Iran a shekarar 2015.

Yayin jawabi ga manema labarai bayan kammala taro, shugaban Amurka Donad Trump, ya yi gargadin cewa zai dauki tsattsauran mataki akan Iran muddin ta sake maido da shirinta na inganta makamshin nukiliya da nufin kera makamai.

Trump na sukar yarjejeniyar da aiki a yanzu da cewa, bata da tasiri akan shirin kera manyan makamai masu linzami da kasar ta Iran ke ci gaba da yi, sai kuma uwa uba karuwar karfin fada aji da take samu a yankin gabas ta tsakiya.

A ranar 12 ga watan Mayu mai zuwa, wa’adin da Amurka ta deba domin sake fasalta yarjejeniyar nukiliyar Iran zai kare, muddin kuma kasashen da ke cikin yarjejeniyar suka gaza yi mata kwaskwarima akwai yiwuwar Amurkan ta janye daga ciki, kamar yadda ta yi barazana a baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.