Isa ga babban shafi
Brazil-Najeriya

Sojin Brazil sun ceto 'yan Najeriya a tsakiyar teku

Sojin ruwan kasar Brazil sun tseratar da wasu tarin ‘yan gudun hijira da suka fito daga Najeriya da Senegal da Guyana da suka shafe kwanaki 35 a tsakiyar teku suna bulayi.

'Yan cirani na halaka a yayin kasadar tsallaka teku da zimmar shiga kasashen Turai
'Yan cirani na halaka a yayin kasadar tsallaka teku da zimmar shiga kasashen Turai ANGELOS TZORTZINIS / AFP
Talla

Rundunar sojin ruwan ta Brazil ta ce mutanen 25 dukkaninsu maza ne kuma sun shafe akalla kwanaki 35 suna bulayi a cikin tekun Amazon kafin daga bisani wasu jami’ansu su gano su.

A cewar rundunar a yammacin Asabar din da ta gabata ne dakarunta na musamman da ke shawagi a cikin ruwan ta hango jirgin ‘yan ci rani wadanda ke cikin galabaita, matakin da ya tilasta wa wani jami’i shiga cikin ruwan don tseretar da rayukansu.

Rundunar sojin ruwan ta Brazil ta ce, bayan isa wajen jirgin ne suka gano ‘yan ciranin guda 25 da kuma wasu ‘yan kasar ta Brazil guda biyu da ake kyautata zaton masu safarar mutane ne.

A cewar Hukumar Kare hakkin Dan Adam ta Maranhao da ke kasar ta Brazil, yanzu haka mutanen 25 na samun kulawar da ta dace a hannun jami’an ‘yan sanda kafin daga bisani a mika su inda ya dace.

Sanarwar ta ci gaba da cewa mutanen biyu ‘yan Brazil za su fuskanci tuhuma, idan kuma aka same su da laifi za ayi musu hukunci dai dai da laifin da suka aikata na cutar da bakin haure.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.