Isa ga babban shafi
Syria-Jordan

Yawan 'yan gudun hijirar Syria ya haura yadda ake tunani- UNHCR

Hukumar kula da ‘yan cirani ta majalisar dinkin duniya UNHCR ta ce adadin mutanen da rikicin Syria na baya-bayan nan ya raba da gidajensu ya tasamma dubu dari hudu ninki uku na adadin da aka bayyana tun da farko.

Muhammad Shamma jagoran masu fafutukar ya ce akwai bukatar gwamnatin kasar ta yi nazari tare da girmama bukatar masu neman mafakar da kuma halin da su ke ciki.
Muhammad Shamma jagoran masu fafutukar ya ce akwai bukatar gwamnatin kasar ta yi nazari tare da girmama bukatar masu neman mafakar da kuma halin da su ke ciki. REUTERS/Loren Elliott
Talla

Kakakin hukumar a Jordan Muhammad Hawar daga litinin din data gabata zuwa jiya juma’a akalla mutane dubu 45 suka fice daga Syrian inda su ke kyautata zaton samun karuwar masu ficewar matukar rikicin ya kara tsananta a kwanakin karshen mako.

Duk da cewa an cimma yarjajeniyar tsagaita wuta a farmakin da dakarun na Syria ke kaiwa kudancin kasar amma ci gaba da zaman dakarun a yankin na matsayin barazana ga ayyukan jinkai a gab da iyakar da ta hada Syrian da kasashen Jordan da Isra’ila.

Kiyasin na UNHRC na zuwa a dai dai lokacin da masu fafutukar kare hakkin dan adam na Jordan ke ci gaba da gangamin neman gwamnatin kasar ta amince da bukatarsu ta ci gaba da karbar ‘yan gudun hijirar Syria da rikici ya raba da gidajensu.

Muhammad Shamma jagoran masu fafutukar ya ce akwai bukatar gwamnatin kasar ta yi nazari tare da girmama bukatar masu neman mafakar da kuma halin da su ke ciki.

Shamma wanda ke jagorantar gangamin tun bayan sabuwar gwamnatin Firaminista Omar Razzaz ya sanar da shirinsu na dakatar da karbar masu neman mafakar ‘yan Syria kan dalilai na tsaro da kuma barazana ga tattalin arzikin kasar, ya ce akwai bukatar gwamnatin ta tuna da dokokin kasa da kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.