Isa ga babban shafi
MDD-AMURKA

Hukumar lafiya ta duniya ta soki kamfanin taba shigari na Amruka PMI

Hukumar lafiya ta MDD (OMS) ta soki kokarin da manyan kamfanonin taba sigari na duniya ke yi wajen sake wa ranar yaki da shan taba sigari ta duniya ma’ana, maimakon ranar nuna illar da shan tabar ke yiwa bani adam.

Sciences_Novembre: Mois sans Tabac
Sciences_Novembre: Mois sans Tabac DR
Talla

Albarkacin wannan rana ta yaki da shan taba sigarin da za ta gudana a ranar juma’a, 31 ga watan mayu 2019 hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da wani kamfen wayar da kanun mutanen duniya, kan mummunar illar da shan taba sigari ke yiwa dan adam.

Hukumar ta MDD ta kuma soki yinkurin da kamfanin Philip Morris International (PMI) ke yi, na samar da tasa ranar yaki da shan tabar a cikin wannan mako, domin tallata sabon nau’in tabar sigarin da ya samar, wacce turiri ne ake zuka ta hanyar wata karamr na’ura mai kama da biro, maimakon zukar hayaki ta bakin wuta, da kamfanin ya gabatar a matsayin masalaha ga rage tasirin annobar ta shan tabar sigarin.

A wata fira da AFP shugaban sashen yaki da shan taba sigarin na hukumar OMS/WHO Vinayak Prasad, ya ce suna kallon wannan yinkuri da kamfanin tabar na kasar Amruka PMI ke yi a matsayin yaudara, domin samun damar ci gaba da saiyar da mummunar hajarsa dake kishe sama da kimanin mutane miliyan 8 a ko wace shekara a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.