rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An samu girgizar kasa a California

media
Yankin California na kasar Amurka www.usgs.gov

An samu girgizar kasa mai karfin maki kusan 6 da rabi a Jihar California dake Amurka wadda ta lalata wani sansanin soji da gidaje, amma ba tare da samun rasa rai ba.


Rahotanni sun ce an ji karar girgizar kasar a birnin Los Angeles mai nisan kilomita 160 da Las Vegas, Jihohi biyu dake makoftaka da California a ranar da kasar ke bikin samun yanci.

Shugaba Donald Trump ya bayyana cewar babu gagarumar ta’adin da aka samu.

Jami’an tsaro na ci gaba da sa idanu don gano wuraren da watakila aka samu barna.