An kori wani jami’in zabe a Liberiya bayan yin coge
Hukumar gudanar zabe a Liberiya ta sallami Jami’in yada labaranta bayan yunkurin aikawa Jam’iyyar Adawa ta CDC ta sakon ita ke kan gaba a zaben shugaban kasa da aka gudanar a 11 ga watan Octoba.A sakon wasikar ta Bobby Livingstone, ya tsara cewa Shugaba Sirleaf ta Jam’iyyar UP ita ke da yawan kuri’u kashi 32.7 amma kuma jam’iyyar adawa ta CDC ke da rinjayen kuri’u tsakanin ta da ‘yan takara 16.Tun da farko Jam’iyyar adawa ta CDC ta yi zargin tabka magudi tare da neman bukatar an sallami shugaban hukumar gudanar da zaben.Wannan zargin kuma na CDC ya kara cusa shakku a cikin kasar da ke kokarin kammala zabe karo na biyu bayan kawo karshen yakin shekaru 14 da ya yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin 250,000.
Wallafawa ranar: