Isa ga babban shafi
Liberiya

Shugaban hukumar Zaben Liberiya ya yi murabus

Shugaban Hukumar zaben Liberiya, James Fromayan, ya sanar da aje aikinsa, sakamakon korafin magudi da ‘Yan adawa suka yi, inda suke cewa rashin sauke shi zai sa su kauracewa zaben shugaban kasa da za’a gudanar zagaye na biyu.A makon jiya Tubman Babban mai hamayya da shugaba Johnson Sirleaf, ya yi barazanar kauracewa shiga zaben idan ba’a samu sauyi ba a shugabancin hukumar zaben kasar.Fromayan, wanda ya musanta zargin da ake masa yace mataimakiyarsa ce Elizabeth Nelson zata karbi aikin shi.A zagayen farko na zaben da aka gudanar a 11 ga watan Octoba, Johnson sirleaf ta lashe kuri’u kashi 43.9, Tubman kuma na Jam’iyyar adawa ta CDC ya samu kuri’u kashi 32.7 wanda hakan ya bada damar shiga zagaye na biyu.Ana tunanin Sirleaf ce zata lashe zaben bayan da tsohon shugaban ‘yan tawaye Prince Johnson wanda ya zo na uku ya bayyana marawa shugabar baya a zaben da za’a gudanar zagaye na biyu. 

Winston Tubman, babban mai hamayya da Ellen Johnson-Sirleaf, lokacin da yake kada kuri'arshi
Winston Tubman, babban mai hamayya da Ellen Johnson-Sirleaf, lokacin da yake kada kuri'arshi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.