Isa ga babban shafi
Gambiya-ECOWAS

ECOWAS zata kaurace wa zaben shugaban kasa a Gambiya

An rufe yakin neman zaben shugaban kasa a kasar Gambiya inda ake shirin gudanar da zaben a gobe Alhamis, Shugaban kasar Yahya Jammeh yana cikin ‘yan takara, amma Jam’iyyun adawa sun hada wani gangamin karshen domin kawo karshen wa’adin mulkinsa a karo na hudu.

Shugaban kasar Gambiya Yahya Jammeh
Shugaban kasar Gambiya Yahya Jammeh Wikimedia Commons
Talla

Kasashen duniya da dama sun zargi shugaba Jammeh da keta hakkin ‘yan kasar karkashin mulkinsa, amma magoya bayansa suna ganin ya samar da abubuwan ci gaba a cikin kasar da suka shafi samar da makarantu da asibitoci.

Mista Jammey ya shaidawa ‘yan kasar a yakin neman zabensa a wa’adi na biyar zai samar da ayyukan ci gaba cikin watanni uku.

Sai dai wasu ‘yan kasar suna ganin har yanzu babu Demokradiyya a cikin kasar domin shugaban ba zai saurari duk wanda bai jefa masa kuri’a ba.

Kasar Gambiya tana makwabtaka ne da kasar Senegal mai yawan mutane kusan Miliyan biyu. Amma Mutane 800,000 ne suka yanki rijistar kada kuria a zaben.

Kungiyar kasashen yammacin Africa ta ECOWAS da ke sa ido ga zaben kasashen, tace bata ga alamun za’a gudanar da sahihin zabe a cikin kasar ba.

Yanzu haka kuma ECOWAS tace ba zata tura jami’an sa ido ba a zaben domin sakamakon binciken da ta gudanar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.