Isa ga babban shafi
Gambiya

Shugaban Gambiya Jammeh ya lashe zabe da kashi 72 cikin 100

Sakamakon zaben kasar Gambiya da aka bayyana yau Jumma’a, ya tabbatar da cewa, Shugaban kasar Gambiya mai barin gado Yahya Jammeh, ya lashe da gagarumin rinjaye na kashi 72 cikin 100, inda ya bada tazara mai yawa a zaben shugabancin kasar da aka gudanar a jiya Alhamis.

Shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh
Shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh Reuters
Talla

Shugaban hukumar zaben kasar Mustapha Carayol ya bayyana cewa Shugaba Jammeh ya samu nasarar wa'adi na hudu na mulkin kasar da kashi 72 cikin 100, yayin da babban mai kalubalantarsa Ousainou Darboe ya samu kashi 17 cikin 100. Hukumar zaben ta ce an samu fitowar masu zabe na kashi 83 cikin 100.

Nasarar ta nuna cewa Shugaba Jammeh zai sake mulkin wannan karamar kasa dake yankin Yammacin Afrika na karin wasu shekaru biyar. Tuni babban mai kalubalantar Shugaba Jammeh, Darboe ya yi watsi da sakamakon zaben.

Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS-CEDEO ya kauracewa tura 'yan kallon zabe, saboda yadda ake tursasa wa 'yan adawa, haka sauran kungiyoyi na kasashen duniya suka kaurace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.