Isa ga babban shafi
AU-Bankin Duniya-Najeriya

Tarayyar Afrika sun goyi bayan takarar Ngozi a Bankin Duniya

Kungiyar Kasashen Afrika ta AU, sun goyi bayan takarar Ministan kudin Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala domin samun shugabancin Bankin Duniya, inda kungiyar ta bukaci duba cancanta wajen zaben wanda zai shugabanci Bankin.

Ngozi Okonjo-Iweala Ministan kudin Najeriya
Ngozi Okonjo-Iweala Ministan kudin Najeriya REUTERS/Nicky Loh/Files
Talla

Ministocin kudaden Nahiyar, tare da takwarorinsu na tsare tsare, a karkashin Fira Ministan Habasha, Meles Zenawi suka bayyana goyan bayansu ga takarar Ngozi a taron da suka gudanar a birnin Addis Ababa.

Gwamnan  babban bankin Najeriya, Sanusi Lamido Sanusi ya shaidawa Rediyo Faransa cewa Ngozi ta cancanci shugabancin Babban bankin saboda kwarewarta a sha’anin tattalin arziki.

A cewar Mista Sanusi, Mukamin babban bankin mukami ne mai matukar muhimmaci ga ci gaban Afrika wajen ba kasashen Afrika bashi kuma mukami ne da ba a taba samun wani daga Afrika ba wanda ya taba shugabancin Bankin.

A karon Farko a bana an samu wasu ‘Yan takara guda biyu wadanda zasu kaluabalanci dan takarar Amurka, Ngozi Okonjo-Iweala ‘Yar Najeriya da Jose Antonio Ocampo dan kasar Colombia.

Sai dai har yanzu Amurka na iya lashe kujerar shugabancin Bankin saboda goyon bayanta ga kasashen Yammaci inda ake has ashen dan kasar Korea ta Kudu ne Jim Yong Kim shi zai gaji Robert Zoellick wanda Amurka ke goyon baya.

Mambobin Kasashe 187 zasu zabi wanda zai gaji Robert Zoellick.
Kamfanin Dillacin Reuters ya ruwaito cewa kasar Brazil zata marawa Ocampo baya wanda Farfesa ne a Jami’ar Colombia a birnin New York.

Okonjo-Iweala tsohuwar Jami’a ce a babban Bankin duniya inda bayan zabensa Shugaban kasa a Najeriya, Goodluck Jonathan ya nemi taimakonta domin karbar mukamin Minista don taimakawa ci gaban gwamnatinsa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.