Isa ga babban shafi
MDD-Afrika

Rikicin Mali, Somalia, G/Bissau da Sudan ne ya mamaye taron MDD da AU

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, da kwamitin tsaro da wanzar da zaman lafiya na kungiyar kasashen Afrika ta AU, sun bukaci shugabanin sojin Guinea Bissau sauka daga karagar mulki, tare da bayyana damuwarsu kan barazanar kungiyar Al Qeada a Mali, da tashin hankalin da ake samu a kasashen Sudan da Somalia.

Dakarun Najeriya da aka aika da su a kasar Guinea Bissau
Dakarun Najeriya da aka aika da su a kasar Guinea Bissau AFP / SAMBA ANTAM BALDE
Talla

Wannan ya biyo bayan wata ganawa da suka yi a birnin New York na amurka, game da halin da ake ciki a kasashen Afrika.

Bangarorin biyu sun yi Allah waddai da juyin mulkin da ake samu a Afrika ta Yamma, inda suka bayyana aniyar tabbatar da demokradiya da wanzanr da tsaro da zaman lafiya a Nahiyar.

A ranar 22 ga watan Maris ne Sojoji suka hambarar da gwamnatin Farar hula ta Amadou Toumani Toure al’amarin da yasa ‘Yan tawaye suka samu damar karbe ikon yankin Arewacin kasar wanda ya fi kasar Faransa Girma.

Mako guda juyin mulkin Mali aka sake samun Juyin mulki a kasar Guinea Bissau a watan Afrilu gab da kammala zaben shugaban kasa.

Akwai damuwa da kungiyoyin biyu suka bayyana game da barazanar matsalar tsaro da ake samu a Yankin Sahel, musamman barazanar kungiyar Al Qaeda da kuma barazanar rikicin Najaeriya na kungiyar Jama’atu Ahlil Sunnah lil da’awati wal Jihad da ake kira Boko Haram .

Taron ya tattauna hanyoyin da za’a bi wajen magance matsalar fashin jiragen ruwa a yankin Yammacin Afrika da yankin Sahel.

Bangarorin biyu yi na’am da matakin komawa teburin sasantawa tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu wadanda suka abka yaki da juna saboda mallakar yankuna masu arzikin Man Fetir bayan samun ‘Yancin yankin kudanci.

Ana dai tunanin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da wakilan kungiyar Tarrayar Turai zasu sake ganawa kafin watan Ylin shekarar 2013.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.