Isa ga babban shafi
Guinea Bissau-Portugal

Gwamnatin G/Bissau ta zargi Portugal da yunkurin juyin mulki

Gwamnatin Kasar Guinea Bissau ta zargi kasar Portugal da Tsohon Firaministan kasar, Carlos Gomes Junior da yunkurin juyin mulki a kasar, sakamakon harin da wasu ‘Yan bindiga suka kai barikin sojin kasar, wanda ya yi sanadiyar kashe mutane shida.

Sojin Guinea Bissau, da ke sintiri a sassan domin farautar wadanda suka kai hari a barikin Soji
Sojin Guinea Bissau, da ke sintiri a sassan domin farautar wadanda suka kai hari a barikin Soji AFP
Talla

Ministan sadarwar kasar, Fernando Vaz, yace wannan yunkurin wani shiri ne da bangarori biyu suka shirya domin kifar da gwamnatin kasar, wanda ke kokarin jefa kasar cikin rudani da kuma dawo da Gomez a kan ragamar shugabancin kasar.

Shaidun gani da ido sun ce Kaftin Pansau N’Tchama, kwamandan zaratan kasar, wanda ya jagoranci kashe shugaban kasar, Joao Bernardo Vieira a shekarar 2009 shi ne ya jagoranci kai hari a barikin Soji, kafin a kore su.

Hukumomin Guinea Bissau sun tabbatar da mutuwar mutane bakwai, sakamakon harin Yan bindigar a barikin na soji.

Rahotanni sun ce, sojin kasar daga bisani sun kaddamar da wani sintiri a daukacin birnin Bissau don farautar maharan, wadanda suka gudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.