Isa ga babban shafi
Masar

‘Yan adawa sun yi kiran gudanar da zanga zanga a Masar

‘Yan adawa a kasar Masar sun yi kiran gudanar da wata Zanga-zanga domin adawa da sakamakon zaben raba gardama da aka gudanar akan sabunta kundin tsarin mulki wanda suka yi zargin an yi magudi. Wasu gungun alkalan kasar sun ce za su kauracewa zagaye na biyu na zaben.

Daruruwan masu zanga a Dandalin Tahrir birnin Alkahira na Masar wadanda ke adawa da sakamakon zaben raba gardama
Daruruwan masu zanga a Dandalin Tahrir birnin Alkahira na Masar wadanda ke adawa da sakamakon zaben raba gardama REUTERS/Amr Abdallah Dalsh
Talla

Yanzu haka kuma babban mai gabatar da kara Talaat Ibrahim Abdallah ya mika takardar murabus dinsa wanda Muhammed Morsi ya nada a watan jiya.

Majalisar kotun Koli tace za ta yi zama na musamman dangane da murabus din babban mai gabatar da karar kafin a je zagaye na biyu na zaben raba gardamar.

Gungun Jam’iyyun adawa sun yi kira ga al’ummar Masar su fito domin neman ‘yancinsu tare da watsi da zaben raba gardamar da za’a gudanar zagaye na biyu bayan jam’iyar Brotherhood ta shugaba Morsi ta yi ikirarin cewar kashi 57 sun jefa kuri’ar amincewa da sabon kundin tsarin mulkin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.