Isa ga babban shafi
Sudan

Gwamnatin Sudan da ‘Yan tawaye sun yi yarjejeniyar tsagaita wuta

A wata sasantawa da aka yi a birnin Doha dake kasar Qatar, kasar Sudan da ‘Yan tawayen kasar na kungiyar JEM, sun saka hanu a wata yarjejeniyar tsagaita wuta, wacce ta fara aiki a daren Jiya Lahadi, kamar yadda kafofin yada labaran kasar ta Qatar suka rawaito Firaministan kasar, Ahmed al-Mahmud na fada.

Shugaban kasar Sudan, Omar Albashir
Shugaban kasar Sudan, Omar Albashir Reuters/Mohamed Nureldin Abdallah
Talla

“Wanna yarjejeniyar za ta bude hanyar tattaunawar gaskiya tsakanin bangarorin biyu.” Inji Mahmud.

Firaministan kasar ya bayyana cewa kasar ta Qatar za ta shirya wani taro a ran bakwai ga watan Aprilu domin neman tallafi ga kasar Sudan, wanda hakan zai taimaka mata wajen farfadowa.

Fiye da shekaru bakwai Kasar Qatar na shiga tsakani a rikicin kasar ta Sudan, inda a watan Yulin shekarar 2011, gwamnatin Sudan ta saka hanu a wata yarjejeniya da wani bangaren ‘Yan tawayen kungiyar Liberation and Justice Movement.

Akalla mutane 300,000 aka kashe a Dafur kana sama da mutum miliyan daya suka fice daga gidajensu tun bayan barkewar rikici tsakanin wadanda ba larabawa ba da hukumomin Khartoum, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.