Isa ga babban shafi
Sudan-MDD

Dubban Mutane na fama da Yunwa a Sudan-MDD

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya na cewa dubban mutane a yankin Kordofan na kasar Sudan na cikin mummunar matsanancin yunwa, da yasa tilas su dogara da ganyaye da itatuwa. Kamar yadda John Ging na Kwamitin Jin kai na Majalisar Dinkin Duniya yace kashi 80 na mazauna yankin kudancin Kordofan, na dogaro ne da cin abinci sau daya rak.

Rikicin Sudan a yankin Darfur yasa mazauna yankunan kudancin Kordofan da Blue Nile, kauracewa gidajensu
Rikicin Sudan a yankin Darfur yasa mazauna yankunan kudancin Kordofan da Blue Nile, kauracewa gidajensu Reuters/Hereward Holland
Talla

Kungiyoyin agaji na cewa akwai bukatar yin wani abu, game da wannan mawuyacin hali da mutanen yankunan kasar ke ciki, kasancewa Gwamnatin kasar Sudan sun haramtawa kungiyoyin taimakawa daga kasashen waje isa yankunan da ake zancen.

A watan Mayun bara ne Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya nemi a bari a kai kayan agaji, tare da barazanar daukan wani mataki.

Yankin Kordofan da yankin Blue Nile na kan iyakan kasar Sudan ne da makwabciyar ta Sudan ta Kudu, a nan ne kuma kazamin fada ya kaure bayan samun ‘yancin kan Sudan ta Kudu a 2011.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya mutane dubu Dari Tara rikicin Sudan ya shafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.