Isa ga babban shafi
Sudan

Sudan za ta bude sabon filin tonon Mai

Kasar Sudan na kokarin bude wani sabon Filin hako Man Fetir a wannan makon, wannan na matsayin wani mataki na kokarin cike gibin da ta samu ta fannin samun kudaden shiga sakamakon ballewar kasar Sudan ta Kudu.Kamfanin dillancin labarai na SUNA ya rawaito shugaba Omar al-Bashir na cewar zasu kaddamar da wannan Filin ne mai suna HADIDA.Filin da aka bayyana tsammanin samun akalla Ganga 100,000 a kowace Rana, na kan iyakar kasar tsakanin Gabashin Darfur, da kuma kudancin Kurdufan, da jihace da tafi samarda albarkatun Man Fetir, a kasar ta Sudan.A halin da ake ciki kuma Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ya bayyana fatan samun damar sake ganawa da shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir, domin kara tattauna batun tsaro da tattalin arzikin kasashen biyu.Omar al-Bashir yace kowane lokaci daga yanzu zai iya tattaunawa da Salva Kiir, domin soma amfani da yarjejeniyar zaman lafiya da wanzuwar tattalin arziki da su biyun, suka sanya hannu a kai, a birnin Adis Ababa na kasar Habasha. 

Shugaban Sudan Omar Al Bashir
Shugaban Sudan Omar Al Bashir
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.