Isa ga babban shafi
Sudan-Sudan ta Kudu

Sudan ta Kudu ta zargi Sudan da kai mata munanan hare-hare.

Sudan ta Kudu ta zargi kasar Sudan da kai wasu munanan hare haren sama kusa da kan iyakar ta, abinda yayi sanadiyar kashe mata soji guda, da kuma raunana wasu guda biyu.

Shugaban kasar Sudan, Omar Albashir (hagu) da shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir (dama)
Shugaban kasar Sudan, Omar Albashir (hagu) da shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir (dama)
Talla

Mai Magana da yawun sojin kasar, Philip Aguer, ya ce wasu jiragen sama masu saukar ungulu biyu ne suka kai harin, da safe, abinda ya ce Sudan ta kudu ba zata amince da shi ba.

Kasashen biyu sun bangare ne a shekarar 2011 inda yanzu haka suke takaddama akan yankin Abyei dake dauke da arzikin mai da kuma batun janye dakarunsu daga kan iyakokin kasashen biyu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.