Isa ga babban shafi
Malawi

Kotun Malawi ta bayar da belin wadanda ake zargin sun ci amanar kasa

Babbar kotun kasar Malawi ta bayar da belin mutane 12 da ake zagin sun yi yunkurin hambarar da gwamnatin shugaba Joyce Banda cikinsu har da kanin tsohon shugaban kasa marigayi Bingu wa Mutharika. Kotun ta nemi mutanen su biya kudi Dalar Amurka 625 tare da mika takardunsu na tafiye taifye ga ‘Yan sandan kasar.

Tsohon shugaban kasar Malawi, Bingu wa Mutharika
Tsohon shugaban kasar Malawi, Bingu wa Mutharika (CC)World Economic Forum/Wikipédia
Talla

Mutanen sun kunshi Ministocin tsuhuwar gwamnatin shugaba Bingu wa Mutharika. Ana zarginsu ne da yunkurin dakile wa Joyce Banda darewa saman kujerar shugaban kasa bayan mutuwar Bingu Wa Mutharika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.