Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Kashi goma cikin dari na 'yan Africa ta kudu na da kwayar cutar HIV

A Afrika ta Kudu, alkaluma da hukumomi kasar suka fitar na nuna cewar kowane daya daga cikin mutane goma a kasar ke dauke da kwayar cutar HIV sai dai kuma an samu raguwar mutuwar mutane sanadiyar cutar . Bayan koma baya da kasar ta samu sanadiyar jan kafa dangane da anobar cutar ta HIV, Afrika ta kudu ta bunkasa, a tsarin ta na yaki da cutar. sabin alkaluma na nuna nasarar tsarin, cutar zata yi sanadiyar mutuwar akalla kaso 32 daga cikin dari a wannan shekarar sabanin kaso 48 cikin dari a shekara ta 2005Shugaban hukumar bicinke kan cutar HIV na kasar, Pali Lehohla ya ce tsarin ya taimaka domin yanzu wadanda suke rayuwa duk da cewa suna dauke da kwayar cutar na da yawa .Ya sanar da cewar kimanin mutane miliyan 5 da digo uku ke dauke da cutar a kasar da ke da al’ummar akalla miliyan 53.Sama da mutane miliyan 1 ne ke kan tsarin shan maganin cutar, a watan Afrilu da ya gabata kamar yadda rahotani suka nuna .Lehohla ya yaba da irin taimakon da hukumomin kasar ke baiwa ma su fama da cutar ta HIV, tare da fatar ganin an yi nasarar samo magani wanan cutar a nan ba da jimawa ba. 

Hoton kwayar cutar HIV
Hoton kwayar cutar HIV DR
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.