Isa ga babban shafi
Saliyo

Tejan Kabbah na Saliyo ya rasu

Tsohon shugaban kasar Sierra Leone Ahmed Tejan Kabbah ya rasu a jiya Alhamis yana da shekaru 82 a duniya, Wanda ake kallon a matsayin wanda ya taka gagarumar rawa wajen dawo da zaman lafiya a kasar da ta share tsawon shekaru tana fama da yakin basasa.

Tsohon Shugaban kasar Saliyo yana Jawabi a lokacin yakin neman zabensa a birnin Freetown
Tsohon Shugaban kasar Saliyo yana Jawabi a lokacin yakin neman zabensa a birnin Freetown AFP/File, Issouf Sanogo
Talla

Kabbah wanda ya mulki kasar Saliyo a tsawon shekaru 10 kafin da kuma bayan yakin basasar kasar da ya yi sanadiyyar mutuwar samar da dubu 120, ana jinjina masa sakamakon shirin kwance damarar ‘yan tawayen da ya kaddamar domin kawo karshen yakin kasar a shekara ta 2002.

Duk da cewa tun a 1968 ne ya shiga harkokin siyasar kasar gadan-dangan, amma sai a shekarar 1996 aka zabe shi a matsayin Shugaban kasar bayan da kungiyar ‘yan tawayen RUF ta Foday Sankoh ta sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a kasar.

Watanni Shida bayan wannan zabe ne sojoji suka tunbuke shi daga karangar mulki, tare da tilasta ma sa yin hijira zuwa makwabciyar kasar Guinea Conakry.

Duk da cewa wanda ya kifar da gwamnatinsa Commander Johnny Paul Koroma ya kulla kawance da tsoffin ‘yan tawayen RUF, hakan bai hana tsohon shugaban Tarayyar Najeriya Janar Sani Abacha aike wa da dimbin sojojin kasar domin dawo da Tejan Kabbah akan karagar mulki ba.

Babu wani karin bayani a game dalilan mutuwarsa, amm tsohon Shugaban ya yi shekaru yana fama da cutar hawan jini.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.