Isa ga babban shafi
Senegal

HRW ta soki Senegal akan almajiranci

Shekara guda bayan da wata gobara ta yi sanadiyar mutuwar wasu Almajirai Takwas a kasar Senegal, hukumar kare hakkin bil’dama da Human Rights Watch tace mahukuntan kasar har yanzu sun kasa daukar matakin hukunci akan wadanda ke cin zarafin kananan yara a makarantun Allo ko tsangaya.

Wani almajiri dauke da kwanon baransa a kusa da babban Masallacin Touba a kasar Senegal
Wani almajiri dauke da kwanon baransa a kusa da babban Masallacin Touba a kasar Senegal AFP/File, Issouf Sanogo
Talla

Kungiyar tace akalla akwai kananan Yara sama da 30,000 a birnin Dakar da ake tilastawa yin Bara. Kuma tun lokacin da aka samu gobarar wuta a unguwar Medina a birnin Dakar, shugaba Macky Sally a sha alwashin daukar matakai.

Hukumar tace dubban yara ne malamansu ke tursasawa yin bara domin kawo na abinci amma gwamnatin kasar ta gaza daukar matakai akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.