Isa ga babban shafi
Malawi

Ana zaben shugaban kasar Malawi

A yau ne ake gudanar da zaben shugbaan kasa a kasar Malawi, inda shugaba Joyce Banda ke fuskantar babban kalu balen zargin cin Hanci da rashawa.Dama dai masu lura da al’amurran Siyasa, sun yi hasashen cewar da kyar zaben na yau bai yi zafi ba tsakanin shugaba mai ci Joyce Banda da wasu manyan ‘yan takara 3 da suka hada da Lazarus Chakwera na Malawi congress party da Peter Mutharika na Cemocratic Progress party da kuma Atupele Muluzi na United Democratic front.Duka duka dai akwai ‘yan takara 12 a zaben na yau da ake gudanarwa, wanda bayanshi kuma, za’a gudanar da na ‘yan Majalisa.Ana kuma sa ran ‘yan kasar Malawi Miliyan 7 da Dubu 400 ne za su jefa kuri’unsu a zaben na shugaban kasa da ‘yan Majlisu kazalika da na Kansiloli.Yanzu haka dai shugaba Joce Banda na fuskantar babban kalubalen zargin cin hanci da rashawa da ya ja hankalin’yan kasar da kuma ake sa ran matsalar ka iya haifar masa koma baya.Amma a inda aka fito Banda ya ta musanta hannu ga wannan badakalar cin hanci da ake mata.Masu kuri’u dai ne za su raba gardama tsakanin Joce Banda da ta hau karagar mulkin kasar bayan mutuwar Bingu wa Muthrika shekaru 2 da suka gabata da kuma abokan hamayyar ta. 

Shugabar kasar Malawi, Joyce Banda
Shugabar kasar Malawi, Joyce Banda
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.