Malawi
Na’urar Kidayar Kuri’un zaben Malawi ta lalace
Na’urar da ake kidayar Kuri’u a kasar Malawi ta samu matsala a lokacin da aka fara kidayar kuri’un zaben shugaban kasa da aka gudanar a cikin wannan makon. Jami’an hukumar zaben sun koma yin amfani da Fax da sakon email wajen tattara sakamakon zaben.
Wallafawa ranar:
Talla
Hukumar zaben tace za’a samu tsaikun fitar da sakamakon zaben da aka gudanar a ranar Talata saboda matsalar.
Zuwa yanzu kuma babu wani sakamako da aka fitar inda Shugaba mai ci Joyce Banda ke takara da Peter Mutharika dan uwa ga tsohon shugaban kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu