Isa ga babban shafi
Malawi

Banda ta soke zaben Malawi

Kasar Malawi ta fada cikin rudanin siyasa bayan shugabar kasar Joyce Banda soke zaben da aka gudanar a makon jiya. Hukumar zabe tace za’a sake bude akwatunan da aka jefa kuri’u bayan an sami magudi a babban zaben kasar da aka gudanar.

Zaben gama gari a kasar Malawi
Zaben gama gari a kasar Malawi afp.com/Gianluigi Guercia
Talla

Magudin da aka samu ya jefa ilahirin kasar cikin zaman zullumi, kuma kamar yadda shugaban Hukumar zaben kasar Maxon Mbendera ke cewa akwai wasu wuraren da aka samu an jefa kuri’u fiye da yawan mutanen da aka yi masu rajistan zaben.

Ya fadi cikin wata sanarwa cewa sun amince tare da sauran jam’iyyun siyasa da ke kasar a sake duba akwatunan da aka jefa kuri’un domin a kara tantance yawan wadanda da aka jefa.

A ranar Assabar da ta gabata Shugaban kasar Joyce Banda ta bayyana soke zaben saboda yawaitan magudi da aka samu.

Uwargida Joyce Banda ta nemi a gaggauta sabon zabe cikin kwanaki 90.

Jim kadan da bayar da sanarwar ne kuma Babban kotun kasar ta zartas da hukuncin hana shugaban kasar soke babban zaben da aka yi, lamarin day a jefa kasar cikin rudanin siyasa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.