Isa ga babban shafi
Malawi

Peter Mutharika ya lashe zaben kasar Malawi

A Malawi, jami’an hukumar zaben kasar sun bayyana Peter Mutharika, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar na ranar 20 ga watan Mayu.A Blantyre cibiyar kasuwancin Malawi ne hukumar zaben kasar ta futar da sakamakon zaben duk da yake ma su adawa da wanan sakamakon suka bukacin a sake kidaya kuri’u.  

Peter Mutharika sabon shugaban kasar Malawi.
Peter Mutharika sabon shugaban kasar Malawi. AFP PHOTO / AMOS GUMULIRA
Talla

Sakamakon zaben na karshe da hukumar ta bayar ya nuna dan takarar jam’iyyar DPP , Peter Mutharika ya sami nasara da kashi 36 cikin dari na kuri’u da aka kada, yayinda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar MCP Lazrous Chakawa, ya sami kashi 29 cikin dari.

Shugabar kasa mai ci Joyce Banda, tazo ta uku da kashi 20 cikin dari.
A yau Asabar ne kamar yada rahotani dake futowa daga kasar Malawi ake sa ran za a rantsar da Peter Mutharika, wanda dan uwan shugaban kasar marigayi Bingu wa Mutahrika ne.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.