Isa ga babban shafi
Najeriya-Kamaru

Sojojin Kamaru sun kashe ‘Yan Boko Haram biyu

Sojojin kasar Kamaru sun yi musayar wuta da Mayakan kungiyar Boko Haram na Najeriya, tare da kashe biyu daga cikin Mayakan bayan sun kai hari a arewacin kasar kamar yadda Gwamnatin Kamaru ta sanar.

Kakakin rundunar Sojin Najeriya, Chris Olukolade.
Kakakin rundunar Sojin Najeriya, Chris Olukolade. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Kakakin gwamnatin Kamaru Issa Tchiroma Bakary yace ‘Yan Boko Haram sun kai harin ne a yammacin jiya Assabar a yankin Mayo Tsanaga a cikin arewacin Kamaru, nan take ne kuma Sojojinsu suka ankara suka fatattaki mayakan tare da karbe motarsu da bindigogi kirar AK 47.

Sai dai kuma gwamnatin Kamaru ba tace ko akwai wani Sojan kasar ba da aka kashe a musayar wutar.

Akwai dai dakaru sama da 1,000 da gwamnatin Kamaru ta jibge a kan iyakarta da yankin arewa maso gabacin Najeriya da mayakan Boko Haram suka addaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.