Isa ga babban shafi
Benin

Interpol ta cafke wadanda ake zargi da fataucin jarirai

Hukumar ‘yan sanda ta kasa da kasa Interpol, ta sanar da cafke wata mata mai suna Safia Koulibaly ‘yar asalin kasar Burkina Faso bisa zargin yin fataucin jarirai, lamarin da yanzu haka ke ci gaba da haifar cece-ku-ce a kasashe da dama na yammacin Afirka.

Fataucin jarirai
Fataucin jarirai
Talla

Safia, wadda ke rike da shugabancin sashen kashe kudade na Majalisar Dokokin kasar Burkina Faso, an cafke ta ne a birnin Cotonou na Jamhuriyar Benin tare da wasu mata mutane 4 da ake zargi da hannu a wannan badakala.

Kwamishinan ‘yan sanda Richard Akodande, ya shaida wa manema labarai cewa suna zargin matar ne da hannu a fataucin jarirai a cikin kasashen yankin cikinsu kuwa har da jariran da ake cewa an sayar wa wasu ‘yan siyasa a Jamhuriyar Nijar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.