Isa ga babban shafi
Masar

Ana tsadar rayuwa a Masar

Mutane Kasar Masar na juyayin halin tabarbarewar tattalin arzikin da ya addabi kasar su abinda ya sa aka samu tsadar rayuwa sabanin yadda akasar take a baya. Rahotanni sun ce kayan abinci da makamashi sun yi tashin goran zabbi inda ‘yan kasar ke cewa gara jiya da yau.

'Yan uwa da dangin magoya bayan hambararren shugaban kasar Masar Mohammed Morsi suna kuka bayan  yanke wa 'yan uwansu da 'yayansu hukuncin Kisa.
'Yan uwa da dangin magoya bayan hambararren shugaban kasar Masar Mohammed Morsi suna kuka bayan yanke wa 'yan uwansu da 'yayansu hukuncin Kisa. REUTERS/Mohamed Abd El Ghany
Talla

Imam Sayeed Inuwa na jami’ar Al Azhar da ke zama a birnin al Kahira yace Talaka yanzu yana mamakin yadda al’amurra suka tarbarbare.

Inuwa wanda yace ya kwashe shekaru 20 a Masar yace a shekarun baya yana da wahala a yi karin farashi a Masar amma lamarin yanzu ya sauya.

Wannan na faruwa ne saboda rikicin siyasa da sauyin gwamnatoci da aka samu a kasar Masar.

A cikin watan Jiya ne Shugaban kasa Abdel Fatah al Sisi wanda ya hambarar da gwamnatin 'Yan Uwa Musulmi ta Mohammed Morsi ya kara fashin Mai, a wani mataki da gwamnatin ta yi ikirarin daidaita tattalin arzikin Masar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.