Tsare minista saboda da zargin cinikin jarirai a Nijar
An cafke ministan noman Jamhuriyar Nijar Malam Abdou Labo, wato daya daga cikin manyan jami’an gwamnatin kasar da ake zargi da hannu a fataucin jarirai.
Wallafawa ranar:
Minista Abdou Labo na daya daga cikin daga cikin mutanen da ake zargin cewa sun yi cinikin jarirai daga wasu kasashe, da suka hada Najeriya, Benin da kuma Burkina Faso.
Kimanin wata daya da ya gabata ne wannan zance ya taso a kasar ta Nijar, kuma tuni aka cafke matan wasu manyan jami’ai na kasar da suka hada da matar Abdou Labo da kuma shugaban Majalisar Dokokin kasar Hama Amadou, wadanda aka ce sun sayo jarirai domin mayar da su a matsayin ‘yayansu daga wadancan kasashe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu