Isa ga babban shafi
Madagascar

Mutane na tagayyara, Yara na wulakanta akan Yunwa a kasar Madagascar

Wani Rahoto da Hukumar samar da Abinci ta Majalisar dunkin Duniya ta fitar na cewar ana wulakanta kananan Yara da yawa, sakamakon matsananciyar yunwar da ta shafi akalla mutane Dubu 200 a kasar Madagascar

Image d’archive d’une précédente inondation à Antananarivo, Madagascar, en 2007.
Image d’archive d’une précédente inondation à Antananarivo, Madagascar, en 2007. AFP PHOTO/GREGOIRE POURTIER
Talla

Ana dai ganin kananan Yara da dama da ka shiga aikin tsince-tsince ragowar abinci a yayin da Iyayensu kuma suka dogara ga tallafin abincin da Hukumar ta Majalisar dunkin Duniya ke rarrabawa.

Rahotanni daga wasu kauyuka da ke yankin kudancin tsibirin da ya fi kowanne girmma a Duniya da ke a kasar ta Madagascar, na cewar tsananin farin da aka yi a Daminar Baraa ne, ya haifar da karancin abincin da a yau al’ummar yankunan ke fama da shi.

Mutane na ta tagayyara, kananan Yara kuma na ta wulakanta, a yayin da Hukumar samar da abinci ta Majalisar dunkin Duniya ke ta kokarin agajin rayuwar mutane Dubu 120 da rashin isasshen Abincin da ya samo asali daga farin da aka sama tsakanin Watannin Okotoba zuwa Fabrarirun Baara da kuma ya lalata kayan Gona ya shafa.

Yanzu haka dai Hukumar samar da abinci ta Majalisar dunkin Duniya ta kaddamar da wani gangamin neman agaji domin samarwa Dubban Daruruwan mutane abinci, a yayin da kuma Yunwa ke masu kisan dauki dai dai.

Ko a shekarar 1991 ma mutane da dama sun mutu sakamakon Yunwa a kasar ta Madagascar, amma inji Rahoton na Hukumar samar da abinci ta Majalisar dunkin Duniya, matsalar Bana kam ba’a magana.

Baya ga matsalar Abincin ma akwai matsalar rashin isassun Ruwan sha da mutane ke fama da ita, mtanen kauyukan kan fita neman Ruwan sha, kuma su mutu a can kamin su iya samun Ruwan da za su sha na wunin, ballantana ma na kaiwa a Gida.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.