Isa ga babban shafi
Indonesia

Kasashen Asiya da Afrika na gudanar da taro a Indonesia

Yau ne Shugabanin kasahsen Asia da takwarorin su na Afirka suka fara wani taron kwanaki biyu a Indonesia a karkashin kungiyar hadin kan nahiyoyin biyu da aka kaddamar a shekaru 60 da suka gabata, kuma ta kai ga kafa kungiyar 'Yan ba ruwan mu, wato Non-Aligned Movement

Shugaban Kasar Indonesia, Joko Widodo, na gabatar da jawaban bude taron
Shugaban Kasar Indonesia, Joko Widodo, na gabatar da jawaban bude taron Reuters/路透社
Talla

An dai kafa kungiyar ne a shekrar 1955 a karkashin shugabancin Sukarno na Indonesia, inda ya samu halartar shugabanin kasashe 30 da suka hada da Firaminsitan India Jawaharlal Nehru da shugaban kasar Masar Gamal Abdel Naseer.

Tuni shugabanin wasu kasashe suka isa Jakarta dan halartar taron wadanda suka hada da shugabanin kasashen China Xi Jingping, Firaminsitan Japan, Shinzo Abe da shugaban Iran Hassan Rouhani.

Shi dai shugaban Kasar Afrika ta Kudu, Jacob Zuma ba zai samu damar halartar taron ba sakamakon rikicin da Kasarsa ke ciki na kai hare hare ga bakin kasashen ketare dake ci rani a Kasar, To saidai ya aika wakilansa.

Taron dai, zai tattauna ne akan samar da zaman lafiya da tsaro da kuma habbakar tattalin arziki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.